Thursday, April 4, 2019

JARUMA NAFISA ABDULLAHI TA YIMA SHUGABA BUHARI KACHA-KACHA


JARIDAR DIMOKURADIYYA:Fitacciyar Jarumar masanaantar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Nafisa Abdullahi wacce aka fi sani da Nafisa Sai Wata Rana ta chachchaki Shugaban kasa Muhammad Buhari game da kashe kashen da ake yi a Jihar Zamfara.

Tace wane irin Shugaba ne wannan zaayi ta kashe Al'ummar da yake Jagoranta amma ya kame bakin sa ana ta kashe su.

Sai wata Rana, tace mutun daya tak aka kashe a kudancin kasar nan amma Shugaban kasa Muhammad Buhari, yana ta Babatu, amma yanzu mutun daya yafi ran Al'ummar Zamfara kenan.

Jarumar ta bayyana haka ne a shafin ta na Twitter, a matsayin martani ga shugaban game da Babatun da yake ta yi kan wani matashi mai suna Kolade Johnson, wanda yansada suka kashe.

Tace koda sau daya Shugaban bai taba nuna alhinin shi ba game da mutanen da aka dunga kashewa a Jihar Zamfara amma yanzu gashi saboda an kashe mutun daya A Yankin kudi Buharin yana ta maganganu.

Monday, April 1, 2019

Mafusata sun dauki doka a hanunsu a jihar ZamfaraBayan kama wani da ake zargin ya na daya daga cikin 'yan ta'addan da su addabi al'uma a karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, wasu mafusatan garin sun dauki doka a hanunsu ba tare da sun mikashi ga hukuma ba.

'Yan kato da gora 'Civilian JTF' wadan da aka fi sani da 'Yan Sakai a jihar ne su ka kama wanda ake zargin a jiya, inda al'uman karamar hukumar su ka yi gaggawa zartas da hukunci ga wanda aka kamar ta hanyar tarwatsa kansa.

Saturday, March 23, 2019

Friday, March 22, 2019

YANDA ZAKA SAMU 1.2GB A LAYIN GLO AKAN #200


Domin samun wannan garabasa kasami layin glo tsoho ko sabo sai ka danna

*777# send


Press 1 send
Press 1send
Press 5send
Press 2send
Press 1send
Shikenan

Domin duba balance

Danna #127*0#

Tuesday, March 5, 2019

Ya kashe dansa saboda ya cinye masa............


Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta kama wani mai suna Okon Emmanuel, bisa zarginsa da kashe  dansa saboda ya shanye faten doyar da aka dafa musu za su ci tare. Wata ’yar sanda mai suna Etebong ta shaida wa manema labarai haka lokacin da take gabatar da wanda ake zargi da sauran wadanda ake zargi  kan laifuffuka daban-daban ga manema labarai a madadin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Austin Agbonlahor, inda Kakakin Rundunar Irene Ugbo ta ce an kama su ne a wurare daban-daban na jihar.

Ana zargin Okon ya kashe dansa ne a Karamar Hukumar Akamkpa ta Jihar Kuros Riba.

Monday, March 4, 2019

YADDA ZA KI SAMU FATA MAI LAUSHI TA HANYA MAI SAUKI

YADDA ZA KI SAMU FATA MAI LAUSHI

Don haka ne a wannan makon zan
kawo miki hanyar da za ki bi wajen samun fata mai laushi ko da fatarki irinta kada ce zatayi laushi acikin dan lokaci.

Kayan Hadi:
-Kabewa
-Yogot
-Sinadarin ‘Mild Freshener-toner’
-kwai
-Zuma
-Auduga

Yadda za a hada:
- Idan fatarki ba bushasshiya ko marar kaushi ko marar maiko ba ce, za ki sanya ta yi laushi kamar haka: Ki samu kabewa sannan ki daka ta, za ki daka har da ‘ya’yanta; daga
nan sai ki dama ta da yogot. Bayan nan sai shafa a jikinki ko fuskarki har zuwa tsawon minti 10 ko 15. Idan ba a samu kabewa ba za a iya daka gurji a hada yogot kafin a shafa a fuska ko jiki.

- Idan kuma bushasshiyar fata ce da ke, bayan kin shafa hadin kabewa da yogot na tsawon minti 10 ko 15 sai ki wanke da ruwan dumi, sannan ki sahafa wani sinadari da ake kira ‘mild freshener-toner’ a jikinki na minti 30 ko awa
guda.

- Idan kuma fatarki mai fitar da maiko ce, sai ki kada kwai, sannan ki samu cokali daya zuwa biyu na zuma, sai ki zuba ruwan lemo tsami kadan, daga nan sai gauraya su, daga nan ki shafa a fuskarki. Amma idan duka jikinki za ki shafa, sai ki nemi kwai da zuma da ruwan jus din da yawa, don ya game miki jikinki. Lokacin da za ki shafa a fuskarki, sai ki kiyaye kada ya shiga idanunki. Hanya mafi sauki ita ce, ki yi amfani da auduga wajen
shafawa a fuska.

KWANKWASIYYA TA RUSHE A KANO KOTU TA KWACEWA ABBA TAKARA TA BAWA IBRAHIM LITTLE.Labari da dumi dumin sa, wata kotun taraiya mai zama a kan titin Court Road dake Kano ta kwace takarar Gwamna daga hannun Abba Kabir Yusuf dan kungiyar Kwankwasiyya inda ta mikawa Alhaji Ibrahim Al-amin Little bisa rashin gaskiya da aka yi wajen zaben fidda gwani na jam'iyar PDP.

Toh tusa fa ta kwacewa bodari, kuma a daidai gabar nan babu wata dama sai dai mu taya mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR murnar lashe zaben sa na ranar asabar.

Alhamdulillah Kano Ta Ganduje Ce!

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
March 4, 2019.

Newsletter

FEATURED POSTS

Facebook