Breaking News

Atiku ya ce zai yi wa wadan da su ka saci kudin Najeriya afuwa

Atiku ya ce zai yi wa wadan da su ka saci kudin Najeriya afuwa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takaran shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam'iyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai yafe wa duk wanda ya saci dukiyar kasa idan ya zama shugaban kasa.

Ya bayyana haka ne a yayin da ya bayyana tare da abokin tafiyarsa, Peter Obi a shirin gidan Talabijin na NTA da a ke hira da 'yan takara wato The Candidate.

Atiku ya ce zai yi wa su wadan dasu ka yi awun gaba da dukiyar kasa afuwa ne domin ko zasu dawo da wasu kudaden da su ka kai kasaahen waje su ka boye.

No comments