Breaking News

Sanata Dino Melaye zai shafe mako biyu a hannun 'yan sanda.

An kai Dino Melaye asibitin hukumar tsaro ta cikin gida (DSS)
Rundunar 'yan Sandan Najeriya ta ce ta samu amincewar kotu kan ci gaba da tsare Sanata Dino Melaye.

Wata sanarwa da ta fitar, rundunar 'yan sandan ta ce kotun tarayya a Abuja ta amince a ci gaba da tsare Dino Malaye har tsawon kwanaki 14 domin gudanar da bincike kan zarginsa da ake yana da hannu a yunkurin kisan dan sanda.

Sai dai ya musanta zargin.

'Yan sandan sun kuma ce ana kula da lafiyar Dino Melaye a wani asibitin gwamnati da ke hukumar tsaro ta cikin gida (DSS) sabanin wasu rahotanni da suka ce an tafi da shi wani wurin da ba a sani ba.

No comments