Breaking News

Kun san me Buhari ke nufi da shekaru 4 masu tsauri?

Abinda Buhari ke nufi da tsauraran shekaru 4 masu zuwa
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar Malam Garba Shehu da wakilinmu Haruna Ibrahim Kakangi:

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya yi wa BBC karin haske dangane da kalaman da shugaban Najeriyar ya yi a kan cewa wa'adin mulkinsa na biyu zai kasance mai tsauri.

Malam Garba ya ce shugaban yana nufin shekaru hudu masu zuwa ga shugaban ba masu sauki bane saboda daga wadannan shekarun babu saura.
Ya ce a fahimtarsa shugaban na nufin zai yi gwaninta ne wajen cika alkawuran da ya daukar wa 'yan Najeriya.
Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da ministocinsa a lokacin da suka kawo masa ziyara a fadar shugaban kasar domin taya shi murnar lashe zaben kasar.

1 comment: