Breaking News

Rashin kafa bazaisa inyi bara ba-Inji wani nakasashe

Nakasa dai a kasar Hausa tazama wata aba wacce ta dabai baye wasu kalilin din mutane guragu, makafi, kurame da sauransu. 
A mafi yawan garuruwan arewacin Nigeria dayawan nakasassu suna bara ne a tituna don neman abincinda zasu ci ko kudaden biyan bukatun yau da kullum. 
Saidai hakan bai hana wasu daga cikinsu fita cikin lafiyayyu don dogaro dakai ba. 
Wannan saurayin matashi dan jihar kebbi ne wanda ya dauki rayuwarsa kacokan zuwa gonar noma shinkafa don kauracewa barace barace.
Yana noma shinkafa da jagindi Saboda rashin kafafu 2 da yayi amma a haka yake noma haryasaba ya kuma maida abin sana’arsa wacce yaki ci yasha har ya samu abin tanadawa rayuwarsa ta gaba. 
Da ace gomnati zata tallafawa irin wadannan matasa nakasassu da sun zama abin alfahari acikin alumma kuma hakan zaisa yan uwansu masu nakasa suji yakamata suma su kama sanaa. 
Wannan dalili yasa muke kira ga nakasasu da su tashi su daure su koyi sanaa bara da roko ba sanaa bace domin tana zubda kima da darajar dan adam.

No comments