Breaking News

YADDA ZA KI SAMU FATA MAI LAUSHI TA HANYA MAI SAUKI

YADDA ZA KI SAMU FATA MAI LAUSHI

Don haka ne a wannan makon zan
kawo miki hanyar da za ki bi wajen samun fata mai laushi ko da fatarki irinta kada ce zatayi laushi acikin dan lokaci.

Kayan Hadi:
-Kabewa
-Yogot
-Sinadarin ‘Mild Freshener-toner’
-kwai
-Zuma
-Auduga

Yadda za a hada:
- Idan fatarki ba bushasshiya ko marar kaushi ko marar maiko ba ce, za ki sanya ta yi laushi kamar haka: Ki samu kabewa sannan ki daka ta, za ki daka har da ‘ya’yanta; daga
nan sai ki dama ta da yogot. Bayan nan sai shafa a jikinki ko fuskarki har zuwa tsawon minti 10 ko 15. Idan ba a samu kabewa ba za a iya daka gurji a hada yogot kafin a shafa a fuska ko jiki.

- Idan kuma bushasshiyar fata ce da ke, bayan kin shafa hadin kabewa da yogot na tsawon minti 10 ko 15 sai ki wanke da ruwan dumi, sannan ki sahafa wani sinadari da ake kira ‘mild freshener-toner’ a jikinki na minti 30 ko awa
guda.

- Idan kuma fatarki mai fitar da maiko ce, sai ki kada kwai, sannan ki samu cokali daya zuwa biyu na zuma, sai ki zuba ruwan lemo tsami kadan, daga nan sai gauraya su, daga nan ki shafa a fuskarki. Amma idan duka jikinki za ki shafa, sai ki nemi kwai da zuma da ruwan jus din da yawa, don ya game miki jikinki. Lokacin da za ki shafa a fuskarki, sai ki kiyaye kada ya shiga idanunki. Hanya mafi sauki ita ce, ki yi amfani da auduga wajen
shafawa a fuska.

No comments