Breaking News

JARUMA NAFISA ABDULLAHI TA YIMA SHUGABA BUHARI KACHA-KACHA


JARIDAR DIMOKURADIYYA:Fitacciyar Jarumar masanaantar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Nafisa Abdullahi wacce aka fi sani da Nafisa Sai Wata Rana ta chachchaki Shugaban kasa Muhammad Buhari game da kashe kashen da ake yi a Jihar Zamfara.

Tace wane irin Shugaba ne wannan zaayi ta kashe Al'ummar da yake Jagoranta amma ya kame bakin sa ana ta kashe su.

Sai wata Rana, tace mutun daya tak aka kashe a kudancin kasar nan amma Shugaban kasa Muhammad Buhari, yana ta Babatu, amma yanzu mutun daya yafi ran Al'ummar Zamfara kenan.

Jarumar ta bayyana haka ne a shafin ta na Twitter, a matsayin martani ga shugaban game da Babatun da yake ta yi kan wani matashi mai suna Kolade Johnson, wanda yansada suka kashe.

Tace koda sau daya Shugaban bai taba nuna alhinin shi ba game da mutanen da aka dunga kashewa a Jihar Zamfara amma yanzu gashi saboda an kashe mutun daya A Yankin kudi Buharin yana ta maganganu.

No comments