Breaking News

MATASAN AREWA KAR KU YADDA DA ZANGA-ZANGA BA MAFITA BANE

Daga Datty Sallafy Kungiyar matasan Arewa karkashin jagorancin Alhaji Nastura Ahmad Sheriff sunyi kira ga jama'ar Arewacin Nigeria su fito zanga-zanga gobe talata Kungiyar sunyi kira da a fito zanga-zangar a jihohi 19 na Arewacin Nigeria saboda matsaloli na tsaro da suka addabi wasu jihohin Arewa Ina kira ga 'yan uwa Musulmai muyi watsi da wannan kira da kungiyar matasan Arewa tayi, domin a zahiri wannan kungiya ba matasan Arewa take wakilta ba, kuma akwai banbancin ra'ayin siyasa a ciki A matsayinmu na Musulmai idan matsala ta addabi al'ummah irin wannan komawa ake ga Allah a duba hukunci da shari'a ya yadda dashi domin neman mafita Maimakon mu biyewa wannan kungiya gwamma mu nemi shawaran a gurin Malamai, sune zasu nuna mana hanyar tsira ba wadanda sukeyi don biyan bukatar kansu ba Duk wanda yace kaje ka aikata wani abu to sai ka duba a matsayinka na Musulmi hakan ya dace da Musulunci ko bai dace ba?. A Musulunci zanga-zanga haramun ne, ba'a kawo gyara da yin zanga-zanga, babu abinda zanga-zanga yake haifarwa face fitina da tashin hankali da kone-konen dukiya da sace-sace da ruguza kasa Irin wanann zanga-zanga da akeso a ingiza matasa rikidewa zaiyi zuwa juyin juya hali, kuma 'yan ta'adda da manyan makiya zaman lafiyar Nigeria zasuyi amfani da wannan damar su jefa sharrinsu, don dama kiris suke jira, gashi ya dace da daidai lokacin da kowa yana cikin bacin rai da haushi, ya kamata mu gane inda ake so a kaimu a baro 'Dan uwa matashi idan Allah Ya kaimu gobe talata ka fuskanci alkibla, ka daga hannunka ka ambaci sunayen Allah Kyawawa, ka yiwa Annabi (SAW) salati, ka yiwa iyayenka addu'ah, ka roki Allah Ya kawo mana mafita akan matsalolin tsaron Arewa wallahi sai yafi tasiri akan yawon zanga-zanga Muna rokon Allah Ya kawo mana mafita na alheri Amin

No comments